Ranan haihuwa

Yau ranan haihuwa na

A yau shekaru na talatin da daya

Ban san a wani lokaci na fita ba

Ko da safe, ko da rana, ko dad’dare

A yau na fadi da ina hanyan zuwa aiki

Ko laifin sabon takalmina ne oho?

Ko laifin dan yayafi da ke sauka da ya sa kasa tayi tsentsi, oho?

Da zan ce wai wani baban fari munafuki ne wanda neke aki da ya mini gaisuwan haifuwa da farko

Amma karya ne

Uwa ta ne ta farko, say kanwa ta, sai munafukin, say ‘yar yapendo ta

Kwanakin da suke wuce sai tunanin Ubana da ya rasu nake yi

Amma a bar maganan sa se waitarana

Mai neke so ma kaina?

Inna so in haifa yara hudu

‘yan biyu da farko ‘yan bude kofan arziki da lafiya

Sai na ukkun mai sani

Sai na huddun ye rufe ta baya

Mu biyar kama tauraro

Sai ikon Allah

Ina son in sami hanyan samu £200, 000,000 a shekara a k'alla

Ina son uwata tai sami rai da lafiya ta ji dandi jikokin da zan baita

Duk mu sami rai dai lafiya

Insha allah

Comments

Popular Posts