*Dan kara zuba kayan dadi akai*

'Dan kara zuba kayan 'da'di akai

Kudin hatsi ya kuma hawa

Ko mutane nawa za su samu rabo a cikin kadan?

Dole a’ 'kara raba nama ‘yan kanana

Kuma a auna mudun cinkafa rabi a cike da kasa

Yara za su ci abinci da kwanu dayya

Ido a bushe, ciki a kumbure



A jika gari say ta kumbura

‘Dan kara zuba sugari akai

Mama ta zaba wa Baba maifi 'kyau duka de muke de shi

Yau zamu ci main shannu da cinkafa?

Wake da mai?

Main ja da gishiri da dumame?



Rago sun bushe

Shannu sai kara lalacewa

Akuyoyi masu fara’a

Aladuna haram


Yaushe za a yi ruwa?

In ji Baba ruwa zai zo

Mama na tsoro kar ruwa ya zo yanzu

Kasa na bukatan ruwa ta tausasa shi

Kasa na bukatan rashin ruwa ta hana ta nutsad da shi a ruwa


Masu sa’a sun samu abinci yau

Wasu da Allah ya so sunna da na gobe

Yara na rawa, yara na wasa, yara na kuka,

Yara na barce, yana sun tashi

Wasu yara kuma sun mutu

Comments

Popular Posts